Connect with us

Jigawa

An sauya ranakun rubuta jarabawar daukar aikin sababbin ‘Yan sanda

Published

on

Rundunar ‘yansandan jihar Jigawa ta sanar da sauya lokacin rubuta jarabawar daukar aikin sababbin Jami’anta.

Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar DSP Lawan Shisu Adam ne, ya bayyana hakan ga manema labarai jiya asabar a birnin Dutse.

Lawan, yace a sabon lokacin da aka sanya an tsara rubuta jarabawar ne cikin kwanaki biyu a jami’ar tarayya dake Dutse, da misalin karfe 8 da 30.

Haka kuma yace wadandan zasu rubuta jarabawar a ranakun juma’a 29 ga watan Oktaba da kuma Asabar 30 ga watan Oktoban 2021, akwai bukatar su sami horo na Kwamfuyuta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!