Labarai
Fursunoni 500 ne ke karatu a jami’ar karatu daga gida ta kasa kyauta
Shugaban jami’ar karatu daga gida ta kasa NOUN Farfesa Abdallah Uba Adamu ya ce akalla Fursunoni 500 ne yanzu haka ke karatu a jami’ar kyauta.
Farfesa Abdallah Uba ya shaida hakan ne lokacin da ya ziyarci babban sakatare a ma’aikatar Ilimi ta tarayya Mr Sonny Echono bisa rakiyar shugabar sashen harkokin ilimi na kasashen rainon Ingila Farfesa Aisha Kanwar.
Ya kara da cewa ko wane dan kurkuku a Najeriya yana da ‘yancin yin karatu kyauta a jami’ar ta NOUN har zuwa inda ya ke bukata.
Tun da fari a na ta jawabi shugabar sashen harkokin ilimi nakasashe rainon Ingila Farfesa Aisha Kanwar, kira ta yi ga hukumomin kasar nan su tura sabon wakilin kasar nan a hukumar sakamkon karewar wa’adin Hajiya Ladi Katagum ta yi.
Da ya ke mayar da martani babban saktare a ma’aikatar ilimi ta tarayya Mr Sonny Echono cewa ya yi sun ware wani kaso na kasafin kudin ma’aikatar na bana don kula da du wasu bukatun ksar nan a sashen ilimi na kungiyar kasashen rainon ingila, kuma shiri ya yi nisa don tura sabon wakilin kasar nan ga sashen.