Connect with us

Kiwon Lafiya

Gamayyar kungiyar kwadagon jihar Ondo ta yi barazanar tsunduma yajin aiki

Published

on

Gamayyar kungiyar kwadago ta jihar Ondo sun yi barazanar tsunduma yajin aikin daga gobe Talata in har gwamnatin jihar ta gazza biyan ma’aikata albashi.

Kungiyar kwadagon ta nemi gwamnan jihar Rotimi Akeredoli da ya iya ma’aikatan jihar Albashin su daga cikin kudin Paris Club da ta karba daga hannun gwamnatin tarayyan a kwanna baya.

 

Wannan na kunshe cikin wasikar da suka aikewa gwamnann mai dauke da kwanan wata na ranr 9 ga wannan watan, kuma mai dauke da sa hannun hadin gwaiwa na shugabanin gamayyar kungiyar kwadagon na jihar Tayo Ogunleye da Soladoye Ekundayo

Ma’aikatar jihar dai na zargin gwamnan jihar Rotimi Akeredoli da rashin tuntubar gamayyar kungiyar kwadagon a lokacin da  gwamnatin tarayya ta baiwa jihar tun da fari kamar yadda aka cimma.

A cewar ma’aikatan jihar ba za’a zauna lafiya ba in har gwamnati ta gazza biyan albashin su daga gobe Talata wajen sake tsunduma yajin aiki kamar na watan Yunin shekara ta 2016.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,433 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!