Labarai
Ganduje: Iyalan da Motar Dangote ta yi sanadiyar rasa rai sun karbi tallafi
Gwamnatin jihar Kano ta baiwa ‘yan uwan Marigayi Nasir Abubakar tallafin kayan abunci wanda Motar kamfanin Dangote tayi sanadiyyar mutuwarsu da iyalinsa a wani hadari a ranar takwas ga watan da muke ciki.
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje wanda shugaban Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano SEMA Kwamared Sale Aliyu Jili ya wakilta.
Alhaji Sale Aliyu Jili ya kara da cewa gwamnatin jihar Kano tayi matukar kaduwa da jin labarin hadarin, hakan yasa gwamnati ta baiwa ‘yan uwansa tallafin kayan abunci da suka hada da Shinkafa buhu biyu ,Gere biyu , Masara biyu, Dawa biyu da kuma Wake biyu.
Da yake jawabi Dagacin garin kuyan Ta’inna dake karamar hukumar Kumbotso Ahmad Abubakar ya yabawa gwamnatin Kano kan wannan kokari na bada wannan tallafi ga iyalan mamacin.
Ilyasu Garba dan uwa ne ga marigayin ya bayyana farin cikin sa bisa tallafin da gwamnatin Kano ta basu a wannan rana.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito dukkanin ma’aikatan hukumar SEMA ne suka halarci garin na kuyanTa’inna domin jajantawa ‘yan uwan mamatan da suka rasu sakamakon iftila’in hadarin da suka gamu dashi a ranar takwas ga watan Maris din da muke ciki.
You must be logged in to post a comment Login