Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kai Tsaye: Gwamnatin Kano ta kafa kwamitoci a kananan hukumomi -Covid 19

Published

on

Yayin kammala jawabinsa, Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce sun kafa kwamitoci na musamman a kananan hukumomi wanda da zarar a samu bullar cutar zasu sanar da hukumomin lafiya don daukar matakan gaggawa.

A cikin jawabin nasa Ganduje ya kuma yi kira ga direbobin mota na jihar kano su rinka fadakar da fasinjojinsu kan kare kansu daga cutar ta Corona.

Daga karshe ya yi kira ga iyaye da su rika tsaftace muhallansu tare da kula da ‘ya’yansu don kaucewar bullar cutar ta Covid 19.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya dakatar da gudanar da taruka a fadar gwamnatin jihar Kano a  matakan da gwamnatinsa ke dauka wajen kare bullar cutar Corona.

Gwamnan ya bayyana hakan a yayin wani jawabi na musamman da ya gudanar a yammacin yau litinin a fadar gwamnatin jihar Kano domin sanar da al’ummar jihar Kano halin da ake ciki dangane da cutar ta Corona.

A yayin jawabin nasa gwanman ya ce ya aikewa masarautun jihar Kano da su sanar da hakimai da dagatai da masu unguwanni kan yadda al’umma zasu kare kansu daga annobar Corona Virus.

Kazalika Gwamnan ya ce gwamanatinsa ta samar da babbar cibiya da za’a killace duk mutumin da ake zargin ya kamu da cutar.

Haka kuma ya ce gwamnatin tarayya ta yi alkawarin za ta karo na’urorin gwaje-gwaje idan bukatar hakan ta taso.

 

Yanzu haka gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya fara gabatar da jawabin na musamman kan annobar cutar Corona Virus.

Gwamna Ganduje ya fara jawabin nasa ne da misalin karfe uku da minti sha takwas na yammacin yau litinin.

Tunda fari da gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa gwamnan zai yi jawabi da misalin karfe 2 na rana.

A cikin jawabin nasa ya bayyana cewa mutanen da suka kamu da wannan cuta a duniya sun haura dubu goma, inda ya ce a babban birnin tarayya mutum goma.

Akan hakan ne ya godewa Allah da ba’a samu bullar cutar ta Covid 19 a nan Kano ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!