Labarai
Ganduje ya daɗe yana yi mun shigo-shigo ba zurfi – Sha’aban Sharaɗa
Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar birni Sha’aban Ibrahim Sharaɗa ya ce, gwamna Ganduje ya daɗe yana yi masa shigo-shigo ba zurfi.
Sharaɗa ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da yayi da Freedom Radio a ranar Lahadi.
Ya ce, kafin ya samu damar ɗarewa kujerar wakilcin ƙaramar hukumar birni sai da Ganduje ya yi ta taɗe shi.
“Tun lokacin da na ƙuduri aniyar shiga siyasa naje wa Ganduje kan ya bani da ma amma sai ya ce ba zan iya ba”.
“Lokacin da aka zo yin zaɓe kuwa wannan lokaci ƙiri-ƙiri Ganduje ya sa ƙafa ya kifar da ni domin ya ɗora Muntari Ishaq Yakasai, ko a lokacin ƙirga ƙuri’u sai da aka riƙa yi mun aringizo”.
Zan yi farin cikin zama gwamnan Kano – Sha’aban Sharaɗa
Sharaɗa ya ci gaba da bayanin cewa “Tun da farko ma sai da Ganduje ya nuna ba zan iya mallakar katin jam’iyya ba, amma da yake dai ba shi ne me yi ba sai ga shi na samu nasara”.
Ya ƙara da cewa “lokacin da aka ayyana Muntari Ishaq Yakasai a matsayin wanda ya samu nasara ban yi ƙasa a gwiwa ba na tafi ƙasa mai tsarki na faɗawa Ubangiji, sai gashi kotun ƙoli ta ayyana ni a matsayin wanda ya ci zaɓe”.
“Ina son mutane su san cewa komai Allah ne yake yi domin kuwa ga shi yanzu ina shugabantar kwamitin harkokin tsaro na najalisar wakilai” a cewar Sha’aban.
Wannan na zuwa ne dai a lokacin da wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar ta APC a Kano bisa jagorancin tsohon gwamna Sanata Ibrahim Shekarau ke fafutukar ganin an kawo gyara ga yadda ake tafiyar da mulkin jam’iyYar a jihar, wadda har ta kai ga an gudanar da zaɓen shugabanci iri biyu
You must be logged in to post a comment Login