Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ku guji bude makarantun Islamiyyu ko kuma ku fuskanci fushin hukuma – Ganduje

Published

on

Hukumar kula da Makarantun Islamiyya da Tsangayu ta Jihar Kano, ta bukaci Makarantun Islamiyya da su guji bude Makarantu domin kaucewa fadawa fushin hukumar.

Shugaban Hukumar Sheikh Gwani Yahuza Gwani Dan Zarga ne ya bayyana haka a yayin da yake zantawa da freedom rediyo.

Gwani Yahuza Gwani Dan Zarga, ya kuma ce rufe Makarantun da budewa yana hannun gwamnatin Jihar Kano, ba wai wasu mutane ba.

Ya kuma ce Malaman Islamiyya masu koyar da tarbiyya, aikin su shi ne umarni da kyakkyawan aiki da kuma hani da mummunan aiki, ba karya dokar gwamnati ba.

Wakilin mu Bilal Nasidi Mu’azu ya ruwaito cewa, hukumar ta umarci wani shugaban Makarantar Salman Bin Faris dake Unguwar Rijiyar Zaki wanda daya ne daga cikin Malaman da suka bude Makarantar da ya bayyana gaban hukumar domin amsa tambayoyi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!