Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu ta dage sauraran karar matar da ake zargi da yanka danta a Kano

Published

on

Babbar kotun jihar Kano dake zaman ta a Miller Road karkashin jagorancin mai sharia Ibrahim Musa Karaye, ta dage ci gaba da sauraran shariar da ake yi ga matar nan da ake zargi da yanka danta, har zuwa ranar hudu ga watan gobe na Oktoba.

Matar da ake zargi da aikata laifin mai suna Saratu Ya’u mazauniyar garin Sabon birni a yankin karamar hukumar Gwarzo, tun a ranar 12 ga watan Yunin shekarar dubu biyu da goma sha takwas aka gurfanar da ita gaban kotun ana tuhumar-ta da laifin yanka danta mai suna Buhari Abubakar mai shekaru biyar.

Lauyan gwamnati Barista Lamido Abba Soron Dinki ya nemi izinin kotu domin a karanta mata laifin da ake zarginta da aikatawa, wanda ba tare da bata lokaci ba ta amince da aikata laifin yanka yaron nata.

Wakilin mu na kotu Bashir Muhammad Inuwa ya ruwaito cewa, lauyan ya nemi izinin kotu da akaita asibiti domin likita ya duba kwakwalwarta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!