Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Ganduje ya kafa kwamiti don kawo sauyi a fannin wasanni

Published

on

Majalisar zartaswa ta jihar Kano ta amince da kafa kwamiti da zai kawo sabbin tsare-tsare tare da sauya salon wasanni don kawo ci gaba a fannin.

Kwamitin da mataimakin gwamna Dakta Nasir Yusuf Gawuna zai jagoranta, zai tabbatar da hadin gwiwa tare dayin aiki kafada-da-kafada tsakanin ma’aikatar wasanni da hukumar kula da harkokin wasanni da kuma ofishin mai bawa gwamna shawara ta musamman a bangaren wasannin.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba ya fitar, ya ce kwamitin zaifi bada karfi ga muhimman bangarorin na wasannin da farfado da makaratar koyar da wasanni dake Karfi a karamar hukumar Garun Malam tare da lalubo hanyoyin samun kudaden shiga a bangaren wasannin.

Malam Muhammad Garba ya kuma ce kwamitin zai kuma taimaka wajen fito da wani tsari da zai baiwa bangarori masu zaman kansu damar daukar nauyin wasannin jihar duk da cewa gwamnati na warewa fannin wani kaso cikin kasafin kudin jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!