Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje ya musanta rahoton jihar Kano ce kan gaba a gurbacewar mahalli

Published

on

Gwanatin jihar Kano ta musanta rahoton da wata cibiya mai suna ‘Airvisual’ ta buga, inda ya bayyana birnin Kano a matsayin birni mafi gurabatar mahalli a Nahiyar Afirka.

Babban sakatare a maikatar muhalli ta jihar Kano, Dakta Garba Sale Ahmed ne ya bayyana haka jim kadan bayyan kammala shirin ‘Barka Da Hantsi’ na nan tashar Freedom Rediyo.

DrGarba Sale Ahmed ya bayyana cewa akwai birane da dama a nahiyar Afirka da suka fi Kano yawan kamfanoni sannan kuma muhalli ta fi ta Kano gurbacewa.

Ya kara da cewa, ba abin mamaki bane idan akwai gurbatar muhalli a Kano amma ba wai a ce Kano ce mafi gurbacewar muhalli ba.

https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2019/11/TRACK-UP-HANTSI-AIR-VISIUAL-HAU-A-15-11-2019.mp3-TRACK-UP-HANTSI-AIR-VISIUAL-HAU-A-15-11-2019.mp3-News.mp3?_=1

Shi kuwa wani masana kan harkokin muhalli da ke jami’ar Bayero a nan Kano Dakta Aliyu Salisu Barau da ya kasance cikin shirin gaskata rahoton ya yi kasancewar abubuwan da rahoton ya bayyana na haddasa gurbatar muhalli duk akwai su.

Batutuwa masu nasaba

Jihar Kano ce kan gaba wajen gurbatar muhalli- Airvisual

Gurbacewar muhalli na na karya tattalin arzikin kasa:Inji farfesa Mustapha Muktar

kafewar da tafkin Chadi ce ta janyo ayyukan ‘yan tada kayar baya a Arewa maso gabashi Najeriya

https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2019/11/TRACK-UP-HANTSI-AIR-VISIUAL-HAU-B-15-11-2019.mp3-TRACK-UP-HANTSI-AIR-VISIUAL-HAU-B-15-11-2019.mp3-News.mp3?_=2

Bakin sun bayyana wannan matsala ba wai ta gwamnatin jihar Kano ba ce kadai, don haka su ma mutane su bayar da gudunmawar don kare jihar daga irin gurbacewar muhalli da ta ke fuskanta.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!