Labarai
kafewar da tafkin Chadi ce ta janyo ayyukan ‘yan tada kayar baya a Arewa maso gabashi Najeriya
Mataimakiyar babban sakataren majalisar dinkin duniya Amina Mohammed ta danganta ayyukan ‘yan tada kayar baya a yakin Arewa maso gabas, kan kafewar da tafkin Chadi ya yi wajen samar da rashin aikin ga milyoyin matasa.
Hajiya Amina Mohammed ta bayyana hakan ne a Stockholm a yayin bude taron makon samar da tsaftaceccen ruwan sha mai taken ‘Ruwan sha da tsirai don cigaban al’umma a duniya’’
Mataimakiyar babbar Sakatariyar ta kuma nuna irin matsalolin da ta fuskanta yayin da take ministar muhalli a Najeriya da kuma lokacin da take shugabar kwamitin samar da tsaftataccen ruwan sha da tsaftar muhalli na majalisar dinkin duniya, tana mai cewa rashin aikin yi ya haifar da matsalolin da irin wadannan yankuna ke fuskanta a duniya.
Ta kara da cewa duk wata al’umma ba zata cigaba ba sai ta inganta rayuwar mata da kuma kare muhalli daga gurbacewa.