Connect with us

Manyan Labarai

Jihar Kano ce kan gaba wajen gurbatar muhalli- Airvisual

Published

on

Rahoton wata kungiya mai zaman kanta mai suna IQ Airvisual ,dake zaman ta a kasar Switzeland ta ayyana jihar Kano a matsayin jiha da ta fi kowacce jihar fuskantar gurbatar muhalli a fadin nahiyar Afrika, wanda mafi yawan gurbatar ke ta’allaka da gurbacewar iska da kimanin fiye da kaso 54 na iskar da ake shaka.

Rahoton ya bayyana cewa abinda ke haddasa yawan gurbacewar iskar sakamakon yawaitar ma’aikatun da ke fitar da hayaki , wasu lokutan kumab dagwalon masana’antu  da kone itatuwa domin samar da gawayi na daga cikin abinda ke haifar da gurbacewar muhallin.

Binciken dai  ya bayyana cewar birnin Kampala na kasar Uganda ce ta biyu bayan jihar Kano.

Sai  Fatakwal dake jihar Rivers wanda ta zo ta uku, sannan Addis Ababa dake kasar Habasha wacce it ace ta zo ta hudu a duk fadin nahiyar Afrika.

Jaridar Kano Focus ta rawaito cewar Kano ce ke kan gaba a jeren jihohin da ke fuskatantar gurbatar muhalli a fadin Duniya, da kimanin kaso 44 cikin dari, sannan kasar Uganda da Habasha.

Kungiyar ta IQ Airvisual ,ta ce nahiyar Afrika na fama da matsalolin gurbatar muhalli sakamakon rashin samun wayar da kai  yadda ya  kamata wajen inganta nahiyar Afrika.

Menene gurbatar muhallin  iska

Gurbatar muhallin iska wani abu  ne da ayyukan dan Adam na yau da kullum ke haifar da shi, wanda yake da illa ga  iska da muke shaka , baya ga kawo cikas da yake yi ga muhalli da muke ciki na yau da kullum.

Bincike ya nuna cewar akalla kimanin mutane fiye da miliyan 3 ne ke mutuwa sakamakon gurbatar muhalli ,musammam ta hanyar iska a duk shekara , walau ta hanyar amfani da itatuwa ko gawayi ko kalanzir da dai sauransu.

Continue Reading

Labarai

WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar bana

Published

on

Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandare ta Afirka ta yamma WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar dalibai dubu casa’in da daya da dari biyu da ashirin da biyar na wadanda suka rubuta jarrabawar masu zaman kansu na  bana a Najeriya.

Babban jami’in hukumar a Najeriya Mr Olu Adenipekun ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar yau, inda ya ce akalla dalibai dubu casa’in da bakwai da tamanin ne suka yi rajistar jarrabawar inda kuma dubu casa’in da hudu da da dari takwas da tamanin da hudu ne suka zauna jarrabawar a kasar nan.

Ya kuma kara da cewa akwai sakamakon jarrabawar dalibai dubu uku da dari shida da hamsin da tara da har yanzu ba a fitar da sakamakonsu ba sakamakon ci gaba da duba jarrabawar da ake yi.

Jami’ar Bayero ta kama dalibai shida da zargin magudin jarrabawa.

BUK ta kori dalibai 63 saboda satar jarrabawa

Hukumar JAMB ta sanar da ranar sake rubuta jarrabawar ga dalibai fiye 12,000

Haka zalika Adenipekun ya bayyana cewa a Najeriya dalibai dubu arba’in da bakwai da dari biyu da talatin da bakwai ne maza yayin da mata suka kasance guda dubu raba’in da bakwai da dari shida da arba’in da bakwai suka zauna rubuta jarrabawar a bana.

Continue Reading

Labarai

Ganduje- mun kammala biyan diyyar aikin gadar Dangi

Published

on

Gwamnatin jihar Kano tace ta kammala biyan dukkannin diyyar gidaje da shaguna daya dakatar da aikin Gadar Sama da kasa dake Titin Dangi dake nan Kano.

Kwamishin ayyuka da raya kasa na jihar Kano Alhaji Mu’azu  Magaji ne ya bayyana hakan yau lokacin fara rushe gidajen da aka kammala biyan diyyar cigaba da gudanar da aikin gadar kasa da dama na Dangi.

Agefe gudu kuma masu gunadanar da sana’oin su a guraran na cigaba da korafi kan yadda aka basu wa’adin kwana guda tak su kwashe kayayyakin su daga wajen don cigaba da aikin.

Gwamnatin tarayya bata gudanar da ayyukan tituna yadda ya kamata ba

Gwamnatin Kano zata cigaba da yada da’awa

Gwamnatin tarayya ta bada hutun Maulidi

A cewar kwamishinan Alhaji Mu’azu Magaji gwamnan kano Abdullahi Umar Ganduje na bukatar ganin aikin gadar ya kammala cikin kankanin lokaci.

Wakilin mu Abdulkareem Muhammad Abdulkareem Tukuntawa ya rawaito cewa, an dai rushe wasu daga cikin gedajen da aikin ya ratsu ta cikin su.

Now Streaming

Freedom Radio Kano
Please wait 20 seconds Or Click on to Play.…

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.