Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Ganduje ya nada mai taimaka masa kan daukar hotuna

Published

on

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sake nada Aminu Dahiru da aka fi sani da Aminu Hikima, a matsayin babban mai taimaka masa kan daukar hotuna.

Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran Gwamnan Kano Abba ya fitar ga manema labarai, inda ya ce nadin ya fara aiki ne nan take.

A cewar Abba Anwar nadin na zuwa ne biyo bayan kotun koli ta tabbatarwa Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje nasarar a jiya.

Ta cikin sanarwar Gwamna Ganduje ya nuna gamsuwar sa da kokarin Aminu Dahiru Ahmad wajen tafiya da zamani a harkokin da suka shafi daukar hoto a zangon mulkin sa na farko.

Gwamna Ganduje ya ce shakka babu, Aminu Dahiru zai zama abin koyi ga sauran matasa kasancewar yadda ya dauki sana’ar daukar hoto da muhimmanci tun kafin nadin nasa.

Ta cikin sanarwar dai, Ganduje ya bayyana hotunan da Aminu Dahiru Ahmad ke dauka a matsayin wanda suka tserewa sa’a, da hakan ya biyo kwarewa da yake a sana’ar daukar hoto.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kuma bukaci Aminu Dahiru Ahmad da yayi aiki tukuru, tare da bayar da tasa gudunmawar wajen ciyar da jihar Kano dama kasa gaba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!