Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Ganduje ya nada sabbin mutum biyu a matsayin masu taimaka masa

Published

on

Gwamnan Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje ya nada sababin  masu  taimaka masa na mussaman guda biyu kan sha’anin tafiyar da harkokin gwamnati.

Daga cikin wadanda gwamnan ya nada akwai Fai’izu Kamaluddeen Na-ma’aji a matsayin mai bashi shawara na mussaman kan al’amuran yau da kullum yayin da kuma ya nada Habibu Abubakar a matasayin babban mai taimaka masa na mussaman kan al’amuran tattalin arziki.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da sakataren yada labarai na gwaman Abba Anwar ya fitar a daren jiya Asabar cewa nadin ya fara aiki ne nan take.

2023: Gadar Ganduje a APC Barau ko Gawuna?

Ganduje ya nada mata masu ba shi shawara guda 5

Ganduje ya nada mace a matsayin shugabar ma’aikata ta Kano

Har Ila yau sanarwar ta kara da cewar Fai’izu  Kamaludden N a-ma’aji wanda aka fi sani da  Fai’izu Alfindiki shi ne tsohon maitaimakawa gwamnan na mussaman kan harkokin wasanni, matasa da al’adu a wa’adin gwamnan na farko kuma manba ne a cibiyar nazarin tattalin arziki na kasa da kasa da siyasa dake zaune a kasar Amurka.

Yayin nadin, gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya umarce su da su amfani da fasahar zamani wajen ayyukan su a matsayin wata kafa na samun cigaban da aka yi  a duniya a ofisoshin su.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!