Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje ya sanya hannu kan dokar ilimi kyauta kuma dole a Kano

Published

on

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu kan dokar ilimi kyauta kuma dole a jihar.

Gwamna Ganduje ya sanya hannun ne a zaman majalisar zartarwar jihar na ranar Laraba.

Dokar na nufin gwamnatin zata hukunta iyayen da ba su sanya ƴaƴansu a makaranta ba.

A yayin zaman majalisar gwamnan ya gabatar da shaidar kammala karatu ga ɗalibai 22 da gwamnatin ya ƙarasa biya wa kuɗin makaranta.

Ɗaliban sun yi karatu a American University Yola, har ma biyu daga cika sun fito da sakamakon matakin farko wato First Class.

Haka ma Ganduje ya rantsar da sabon babban sakatare guda ɗaya Sani Abdullahi Ƙofar Mata.

Sannan ya rantsar da Bala Lawan Gezawa a matsayin kwamishina a hukumar zaɓe ta jiha.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!