Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje ya zargi ‘yan siyasa da haifar da rikice-rikice a yayin Zaɓuka ba Hukumar INEC ba

Published

on

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya kawar da laifin tashe-tashen hankulan zaɓe Daga INEC, Inda ya nuna yatsa ga ‘yan siyasa a ziyarar da tawagar tantancewar hukumar zabe ta kasa zuwa APC. hedkwatar Abuja A Yau Laraba.

Ganduje ya bayyana cikin kakkausar murya, “Na san daya daga cikin manyan matsalolin INEC wajen gudanar da zabe shi ne rashin tsaro, Kowa zai ce INEC, Amma ‘yan siyasa ne.” Ya yi kira da a kara fahimtar dokoki da ka’idojin zabe, inda ya bukaci a ci gaba da wayar da kan ‘yan siyasa don bunkasa yanayin siyasa mai wayewa.

Yayin da yake jaddada buƙatar yin amfani da tsarin mulki na zamani, Ganduje ya jaddada cewa haɗin kan ‘yan siyasa na da matukar muhimmanci domin hana taɓarɓarewar Harƙoƙin zaɓe.

Ganduje, Wanda ya yabawa jami’an Hukumar ta INEC kan ziyarar, ya bayyana cewa jam’iyyar APC za ta yi aiki a duk shekara ba kawai a lokacin zabe ba.

Shugaban jam’iyyar ta APC ya bayyana cewa, “Mun kuma bada umarnin cewa dukkan ofisoshin jam’iyyarmu tun daga unguwanni, ƙananan hukumomi, shiyya-shiyya, har zuwa jahohi, dole ne a samu jami’ai. Kuma a aikace dole ne ofishin ya kasance yana aiki ta yadda zamu wanzu ta fuskar jiki da aiki.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!