Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Kotu ta janye belin Dr. Idris Dutsen Tashi da ta bada

Published

on

Kotun Shari’ar Musulunci a jihar Bauchi ta mayar wa da waɗanda suka tsaya wa Malamin nan Dakta Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi takardun kadarorinsu da suka bayar domin karɓar belin shi da ta bayar a baya.

Wannan mataki dai na da nufin kotun ta janye belin da ta bayar kan Dakta Idris, wanda kuma hakan ke nufi a kowanne lokaci za a iya kama shi kamar yadda lauyan da ke kare shi ya bayyana.

Ana dai tuhumar Dakta Idris ne da laifuka biyu, da suka haɗar da kalaman batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W, samnan ana tuhumarsa da laifin tayar da zaune tsaye.

Kawo yanzu dai ba a fara sauraren wannan shari’a ba kan waɗannan tuhume-tuhume.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!