Connect with us

Kasuwanci

Ganduje : za mu farfado da kadadrorin gwamanti don samun kudin shiga

Published

on

Gwamantin jihar Kano ta jaddada aniyarta na ci gaba da farfado da tare da inganta kadarorin gwamnati da aka kyalesu ba a amfani dasu tsawon lokaci domin samun kudin shiga.

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan yayin gabatar da taron majalisar zartarwa na mako-mako, inda ya karbi bakuncin kamfanoni guda biyu dake neman hadin gwiwa da gwamnatin domin inganta wasu kadarorinta.

A cewar sa, tuni aka samu kamfani na farko da ya gabatar da kudiri akan neman hadin gwiwa da gwamnatin Kano wajen mayar da kamfanin Triumph kasuwar ‘Yan canji.

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kuma godewa ma’aikatar ilimi mai zurfi da lafiya da muhalli bisa ga yadda suka jajirce wajen ganin yara sun koma makaranta.

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa, gwamna Ganduje kafin fara taron majalisar zartarwar a yau, sai da ya mika motar agajin gaggawa ga daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Kano wadda Alhaji Aminu Dantata ya bada tallafi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!