Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje zai ƙulla alaƙa da ƙasar Denmark domin sarrafa shara zuwa dukiya

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce, ta shirya tsaf don ƙulla alaƙa da ƙasar Denmark domin sarrafa shara ta zamo dukiya.

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan lokacin da ya karɓi baƙuncin jakadan Denmark a Najeriya Mr. per Christensen.

Wannan na cikin sanarwar da mai magana da yawun ma’aikatar muhalli Sunusi Ƙofar Nai’sa ya rabawa manema labarai.

Sanarwar ta ce, gwamnan ya buƙaci masu zuba hannun jari da za su shigo ciki wajen gudanar da aikin.

“A yanzu ƙulla alaƙa da ƙasashe ya zama dole domin sarrafa shara ta zamo dukiya kamar su taki da samar da wutar lantarki”.

“Babu shakka jihar Kano ita ce jiha mafi yawan jama’a a Najeriya kuma Kano birni ne na biyu mafi girma a ƙasar, kuma a duk inda kake da yawan jama’a, ɗaya daga cikin batutuwan da ya kamata a magance shi ne matsalar shara domin yawan mutane na haifar da yawan shara”.

Mun daɗe muna ƙoƙarin ganin yadda za a magance matsalar shara, amma sai muka ga babu mafita fa ce mu nemo ƙasashe don ƙulla alaƙa da su”.

Da yake jawabi tun da farko, kwamishinan Muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso, ya ce karamin ofishin jakadancin Denmark ya ziyarci wasu cibiyoyi na kamfanin da gwamnati ta fara ƙulla yarjejeniya da shi ciki har da cibiyar sarrafa shara da ke Zaura.

Kwamishinan ya bayyana ƙoƙarin da gwamnatin tayi na ƙulla yarjejeniyar damar sarrafa sharar ta zama dukiya, har ma aka ware hekta 500 na fili da za a riƙa zuba sharar don sarrafawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!