Labarai
Ganduje zai bibiyi kwangilar gina hanyoyi na 5Km da Kwankwaso ya yi
Majalisar zartarwar jihar Kano ta amince da kafa kwamitin da zai yi nazari kan hanyoyin kilomita 5 dake kananan hukumomin jihar da nufin sake musu fasali ko a kammala su ko kuma a soke kwangilar gaba ɗaya.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a yau Lahadi, lokacin da yake zantawa da manema labarai a wani ɓangare na abubuwan da majalisar ta zartar a zaman da tayi cikin makon da ya gabata
Ya ƙara da cewa, majalisar zartarwar ta amince da soke kwangilar gina tagwayen hanya mai tsawon kilomita 5 a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa da sake bada aikin ga wani kamfani akan kudi fiye da naira miliyan 651
Muhd Garba ya kuma ce, majalisar ta amince da kafa kwamitin da da zai tabbatar da yadda ma’aikatu da hukumomin gwamnati zasu bada goyon baya da hadin kai don samun daidaito wajen aiwatar da dokar haraji da nufin inganta samar da kudaden shiga.
Wakiliyar mu Zahra’u Nasir ta rawaito cewa kwamishinan ya ce, majalisar zartarwar ta amince da sakin kuɗi naira miliyan 20 domin inganta cibiyoyin ci gaban mata dake sabbin masarautu hudu don tallafawa mata da sana’o’in dogaro da kai.
You must be logged in to post a comment Login