Labarai
Ganduje zai yi wa matsalar ruwan sha a Kano diban karen mahaukaciya
Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci ƴan kwangilar da ta bai wa ayyuka da su yi duk mai yiwuwa wajen kammala a yyukan a lokacin da aka ɗibar musu.
Gwamnan Kano Dr Abdullahi Ganduje ne ya bayyana hakan yayin da ya ziyarci tashar samar da wutar lantarki dake Chalawa.
Gwamna Ganduje ya ce, tashar da zata samar da wutar lantarki da zata bai wa gidan ruwa na Challawa da Tiga wutar lantarki, wanda zai taimaka wajen samar da ruwan sha a jihar Kano baki ɗaya.
Da yake jawabi a yayin duba aikin, kwamishinan ma’aikatar ayyuka na Kano Idris Garba Unguwar Rimi ya ce, da zarar an kammala aikin babu shakka matsalar ruwa zata yi sauƙi sannan zai taimaka wajen samar da hasken wuta a fitilun kan titunan Kano domin samar da tsaro.
Wakiliyar mu Zahra’u Nasir ta rawaito cewa, kafin ziyarar ta Challawa, sai da gwamnan ya ziyarci duba aikin kotun gudanar da tarukan da suka shafi harkokin shari’a da ake gudanarwa a sakatariyar Audu Bako (ceremonial court).
You must be logged in to post a comment Login