Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yanzu-yanzu: Majalisar dokoki ta amincewa gwamna Ganduje ya ciyo bashin Naira biliyan 4

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince wa gwamna Ganduje ya ciyo bashin naira Biliyan 4.

Bashin za a fito shi ne domin kammala aikin samar da wutar lantarki mallakin jiha.

Amincewar ta biyo bayan wasiƙar da gwamnan ya aike wa majalisar.

A zaman na Larabar nan shugaban majalisar Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ya karanta takardar.

wadda a ciki gwamnan ke cewa “za a yi amfani da kuɗin ne don kammala aikin samar da hasken lantarkin daga dam ɗin Tiga da kuma na Challawa domin yin amfani da wutar wajen sanya ta a asibitoci da fitilun titi da kuma gidajen ruwan a jihar”.

Sai dai bayan tafka muhawara ne ƴan majalisar suka amince da buƙatar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!