Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje zai gabatar da Ahmad Musa a matsayin dan wasan Kano Pillars

Published

on

Mai magana da yawun Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars , Rilwanu Idris Malikawa Garu, ya tabbatar da cewar, gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje , na daf da gabatar da Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles Ahmad Musa , a matsayin sabon dan wasan tawagar Kano Pillars.

A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar Kano Pillars, Suraj Yahaya Jambul ya fitar mai dauke da sa hannun jami’in yada labarai na kungiyar, Lurwan Idris Malikawa wanda aka wallafa a shafin Internet na Kano Pillars, ,ta ce hakan ya biyo bayan, yarjejeniya tsakanin dan wasan da tawagar ta Pillars , wacce kamfanin Shirya gasar Firimiyar Najeriya (LMC), ya jagoranta.

Sanarwar ta kara da cewa, kamfanin na LMC bisa takardar da shugaban gudanarwar sa Malam Salihu Abubakar ya sakawa hannu ta tabbatar da daukar dan wasa Ahmad Musa, a matsayin babban dan wasa jagora kana kuma Jakadan gasar , zuwa karshen kakar wasa ta 2021.

Daga cikin Yarjejeniyar da aka cimma da dan wasan a cewar Malikawa, ta hada da amincewa dan wasan ya koma duk tawagar da ta nemeshi a fadin Duniya, da zarar ya samu hakan a kowanne Lokaci.

“Muna murna da dawowar dan wasan mu Ahmad Musa, daman namu ne zamu ci gaba da bashi goyon baya da taimaka masa a ko da yaushe a duk inda ya samu kansa”

“Haka zalika muna yi masa addu’ar Allah ya yi masa jagoranci a dukkan Lamuran sa” inji Lirwanu Idris Malikawa.

Ahmad Musa, ya wakilci Kano Pillars a shekarar 2009, inda ya kare kakar wasa ta shekarar a matsayin dan wasan da yafi kowa zura kwallaye. Inda ya zura Kwallaye 18, kafin ya koma taka Leda a tawagar VV Venlo dake kasar Holland (Netherland).

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!