Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ana zargin jami’in KAROTA da kashe wani magidanci a Kano

Published

on

An zargi wani jami’in KAROTA da cakawa wani magidanci wuka a Shataletalen sansanin Alhazai na Kano.

Magidancin dan kimanin shekaru 35 da haihuwa mai suna Mustapha Muhammad ya rasa ransa bayan da jami’in KAROTAN ya caka masa wukar.

Al’amarin ya samo asali ne a lokacin da jami’in KAROTAN ya zargi dan Adaidaita sahun da tsallake layi.

Abinda ya kuma janyo cacar baki tsakanin jami’in na KAROTA da mai babur din Adaidaita sahu.

Daga nan kuma dan KAROTA ya zaro wuka tare da cakawa marigayin wanda ya je wurin domin sullhunta mai babur din da dan KAROTA, kamar yadda dan uwan marigayin mai suna Bello Haruna ya bayyana.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar KAROTA, Nabulisi Abubakar kofar Na’isa ya ce “Mun samu rahoton afkuwar lamarin kuma yanzu haka ‘yan sanda na cigaba da gudanar da bincike.”

“Kamar yadda yake a tsarin gudanarwar aikin hukumar KAROTA ba ma yin magana idan abu yana gaban binciken ‘yan sanda,” a cewar Nabulisi Abubakar.

Haka zalika shi ma mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa shima bai ce komai ba a kan batun.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!