Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje zai mayar da dajin Falgore wurin atisayen sojoji

Published

on

Gwamnatin jihar Kano, zata kashe sama da naira miliyan dari biyar don fara gini tare da samar da sauran kayan ayyuka na gina gurin atisayen Soji a Dajin Falgore.

Gwamna Abdullahi Ganduje, ne ya bayyana haka a yayin taron aza harsashin fara gina wajen atisayen Sojin.

A wata takarda, da sakataren yada labaran gwamna Abba Anwar, ya sakawa hannu aka rabawa manema labarai, ta ambato gwamna Ganduje, yana cewa kasancewar Dajin zamar wata mafaka ta yan ta’adda, da barayin Shanu, masu sata da garkuwa da mutane da yan fashi, ya sanya gwamnatin ta ga dacewar kafa sansanin wanda idan aka kammala shi zai taimaka wajen ragewa ko dakile aikin ‘yan ta’addan.

Karin labarai:

Ganduje zai fara gurfanar da iyayen almajirai masu bara a gaban kotu

Inda Ranka: Alarammomi sun mayarwa Ganduje martani

Gwamna Ganduje, ya ce shirin ya kunshi dukkan jami’an tsaro, da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro don samun kyakyawar alaka, wanda hakan ta sa gwamnatin ta bada na’ura ta manhaja daya, da za a dinga tattara bayanan sirri, tare da ofishin bada izini da kuma shiri a waje daya don lura da al’amuran tsaro a fadin jihar.

A nashi jawabin ministan tsaro na kasa janar Magashi mai ritaya, yace aikin ya yi dai-dai da kudurin gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, na samar da tsaro tare da inganta shi don samar da zaman lafiya mai dorewa, a gefe guda kuma aikin zai samar da tsaro ba ga yankin kadai ba, har ma da bunkasa harkokin tattalin arzikin yankin.

Taron ya samu halartar, manyan jami’an Soji, da yan sanda, da jami’an tsaro daban-daban, sai majalisar wakilai ta samu wakilncin dan majalisa mai wakiltar Doguwa da T/Wada, Alasan Ado Doguwa, da kuma wakilcin Majalisar jihar Kano, karkashin Salisu Riruwai, da sauran masu rike da masarautu na gargajiya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!