Labaran Kano
Ganduje zai fara gurfanar da iyayen almajirai masu bara a gaban kotu
Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje yayi alkawarin fara gurfanar da iyayen yaran dake bara a gaban kotu.
Cikin wata sanarwa mai dauke da sahannun sakataren yada labaran gwamnan Kano Abba Anwar, ta bayyana cewa gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron raba takardun daukar aiki ga malaman da suka bada gudummuwa ta sa kai, ga makarantun Firamare a Kano.
Sabbin malaman makaranta dubu bakwai da dari biyar 7,500 suka karbi takardar daukan aiki daga gwamnatin Kano, a yau Talata.
Ganduje ya kara da cewa, gwamnatin sa ta haramta yin bara a Kano baki daya, kuma gwamnati ta shirya tsaf domin gurfanar da iyayen yaran da aka samu suna bara a gaban kotu.
Gwamna Ganduje ya kara da cewa sakamakon tsarin gwamnatin Kano na ilimi kyauta kuma dole, za’a zamanantar da harkar karatu ta tsarin almajirci.
A karshe Gwamnatin Kano ta ce zata rarraba malamai 7,500 da ta dauka zuwa makarantu tsangayu da kuma na boko.
Labarai masu alaka:
Majalisa ta amince Ganduje ya nada sabbin masu ba shi shawara
You must be logged in to post a comment Login