Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje zai tallafawa kungiyar Akantoci da cibiyar bada horo a Kano

Published

on

Kungiyar Akantoci ta kasa ta ce, zata yi nazari akan ayyukan ta da nufin kawo gyara don kawo cigaba a kasar nan.

Shugaban kungiyar na kasa Muhammad Mainoma ya bayyana hakan a yau ya yin ziyarar da ya jagoranci ‘ya’yan kungiyar zuwa fadar gwamnatin Kano a yau.

Muhammad Mainoma ya kuma bukaci gwamnatin Kano da ta tallafa musu wajen samar da cibiyar da zata rika horar da Akantoci masu tasowa anan Kano.

Mainoma ya kara da cewa sun zo Kano ne domin gudanar da taron tunatarwa akan ayyukan su, wanda zai mayar da hankali akan abubuwan da suka shafi gwamnatin kwarai da auyukan ta.

Ana sa bangaren gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce zai duba bukatun su wajen ganin ya taimaka wa kungiyar don samar musu da cibiyar anan Kano.

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa gwamna Ganduje  ya kuma karbi bakuncin tawagar makarantar koyar da hafsoshin soji ta Jaji a fadar sa.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!