Labarai
Ganduje zai yi ganawar sirri da masu ruwa da tsaki a Kano kan harkokin siyasa

Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, zai fara ganawa da masu ruwa da tsaki dan neman shawarwari a kan sabbin sauye-sauyen siyasa da ke faruwa a Jihar Kano.
Wata sanarwa da Shugaban Ma’aikatan tsohon Shugaban na APC, Malam Muhammad Garba, ya sanya wa hannu ta ce mutanen da Ganduje zai gana da su sun hada da shugabannin jam’iyya da sauran manyan masu ruwa da tsaki, da nufin duba yanayin siyasar da ake ciki da kuma karfafa hadin kai a cikin jam’iyyar.
Sanarwar ta kara da cewa wadannan shawarwari wani bangare ne na kokarin da Ganduje yake yi don hada kai a jam’iyyar APC, musamman a Jihar Kano.
Sai dai kuma sanarwar ba ta ce uffan game da rade-raden da ake yadawa cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, yana shirin sauya sheka zuwa APC.
A Jiya Asbar ne dai tsohon Shugaban na APC ya dawo Najeriya bayan ya kwashe makwanni yana hutu a Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa.
You must be logged in to post a comment Login