Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƙungiyoyi sun bukaci a kama tsohon Gwamnan Kano bisa kalaman tunzuri

Published

on

Ayayin addu’a ta musamman da zanga-zangar lumana da Masu ruwa da tsaki a jihar Kano suka shirya kan rashin adalci sun bukaci hukumomin tsaro da su gaggauta cafke shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje bisa zargin tunzura jama’a.

An yi wannan kiran ne a yayin wata zanga-zangar lumana da addu’a ta musamman da masu ruwa da tsaki a kan rashin adalci suka shirya, karkashin jagorancin Dakta Idris Salisu Rogo, a karamar hukumar Rogo ta jihar Kano.

Gamayyar ta nuna damuwarta kan takun sakar shari’a da ake ta tafkawa a zaben gwamnan jihar Kano, lamarin da ke nuna shakku kan rashin nuna son kai da tsaka mai wuya a bangaren shari’a.

Sun yi karin haske kan al’amuran da jiga-jigan jam’iyyar APC da suka hada da shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, suka yi bayani game da sakamakon hukunce-hukuncen kotuna wanda daga baya ya yi daidai da hukuncin kotun.

Kungiyar ta kuma nuna fargaba kan wasu shirye-shirye a cikin jam’iyyar APC na yin tasiri a shari’ar zaben gwamnan Kano ta bangaren shari’a, da ake zargin cewa za’a bawa Shugaba Tinubu damar sake tsayawa takara a 2027.

Sun kuma jaddada bukatar kotun kolin Najeriya ta tabbatar da adalci ta hanyar tabbatar da cewa wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano a 2023, Abba Kabir Yusuf ne.

Bugu da kari, sun bukaci bangaren shari’a da su kare martabar da suke da ita ta hanyar hana wadanda ke da alaka da cin hanci da rashawa ta’ammali da su ba.

Kungiyar ta jaddada cewa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu zai iya samun goyon bayan al’ummar Kano ne kawai ta hanyar bin adalci da kuma ci gaba da nuna rashin son kai a hukuncin da kotun koli ta yanke kan Kano.

Sun bayyana gamsuwarsu da yadda shugaba Bola Tinubu yake da niyyar tabbatar da dimokuradiyya tare da bukace shi da ya kiyaye ka’idojin adalci.

Bugu da kari, sun yi gargadin cewa duk wani yunkuri na murde wa’adin Abba Kabir Yusuf zai iya kawo cikas ga tsaron kasa, lamarin da ya kamata ƴan Najeriya masu kishin kasa su yi kokarin gujewa.

Taron mutane sama da dubu dari a filin Idi na Rogo an gudanar da addu’o’i na musamman da muzaharar lumana domin nuna goyon bayansu ga gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf gabanin hukuncin kotun koli.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!