Labarai
Garin Gwanda na cikin tsaka mai wuya- Dagacin garin
Al’ummar karamar hukumar Danbatta suna kira da gwamnatin jihar kano data kawo musu dauki a garin Gwanda dake karamar hukumar Danbatta.
Kiran ya fito ne ta bakin wakiln Dgacin garin Malam Sule Hamza Gwanda wanda yake magana da yawun su, yana mai cewa suna fama da matsalar rashin hanya da makaranta da asibiti da wutar lartarki da kuma ruwan sha.
Wakilin dagacin ya kara da cewa suna tafiya tsawon kilomita goma sha biyar a wannnan hanya kafin su shigo cikin garin Danbatta haka kuma asibitinsu ya lalace sosai babu kayan aiki aciki.
Wasu mazauna garin na Gwanda dake karamar hukumar Danbatta sun bayyana mana cewa ‘yan siyasa suna musu alkawari zasu yi musu aiki idan sun zabesu amma har yanzu ba wani abu da suka musu a wannnan gari na Gwanda dake karamar hukumar Danbatta.
Wakilin dagacin garin na Gwanda Malam Sule Hamza Gwanda yace kiran ya zama wajibi duba da cewa kamar gwamnati ta mance da su.
Gwamnatin Kano ta tuhumi shugaban asibitin Rimingado
Gwamnan Jihar Borno ya kai ziyara asibitin kwararru na Umaru Shehu
Wakilin mu Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa al’ummar garin suna kira da ‘yan majalisa na yankin da Shugaban karamar hukumarsu da su mai da hankali wajen samawa jama’ar garin kayayyakin don bunkasa yanki da ma karamar hukumar Danbatta baki daya.