Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majiyyanta sun roki gwamnati  data mayar da wankin koda  kyauta a Kano

Published

on

Wasu majiyyata ciwon koda  a asibitin Koyarwa na Aminu, sunyi kira ga gwabnatin jihar Kano data duba yuwuwar yin aikin ciwon koda kyauta  duba da kasancewar cutar mai saurin talauta al’umma ce.

Wakilin mu Aminu  Audu Baka noma ne ya tattauna da wadannan majiyyata da ke cikin asibitin aminon ya kuma bayyana tattaunawar kamar haka.

Wani majinyaci dake jiyya asibitin na Aminu Kano yace saboda  yanda cutar take cin kudi yasa har sai da ya sayar da gonar gadonsu guda biyu don ganin samun sauki daga cutar.

Akwai bukakatar samar da tsarin bada lafiya mai nagarta ga marasa lafiya-hukumar asibitoci

Jihar Jigawa ta yi wa Kano fintinkau a taimakawa marasa karfi

Abubuwan da ya kamata ku sani gami da lafiyar Idanu

Haka zalika wani majiyyaci ya bayyana  cewa wannan  shine karo na goma sha biyu da akeyi masa aikin gashin koda,  wanda yakan  kashe naira  dubu goma sha bakwai da naira dari a duk lokacin da za’a yi masa aikin.

Mjiyyacin ya kuma mika rokonsa ga gwamnatin jahar Kano data karo injinan  gashin koda, wadanda  zasu wadata a asibitin  kasancewar  inji guda daya ne tak a ake amfani da shi asibitin.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!