Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Garin Gwanda na cikin tsaka mai wuya- Dagacin garin

Published

on

Al’ummar karamar hukumar Danbatta suna kira da gwamnatin jihar kano data kawo musu dauki a garin Gwanda dake karamar hukumar Danbatta.

Kiran ya fito ne ta bakin wakiln Dgacin garin Malam Sule Hamza Gwanda  wanda yake magana da yawun su, yana mai cewa suna fama da matsalar rashin hanya da makaranta da asibiti da wutar lartarki da kuma ruwan sha.

Wakilin dagacin ya kara da cewa suna tafiya tsawon kilomita goma sha biyar a wannnan hanya kafin su shigo cikin garin Danbatta haka kuma asibitinsu ya lalace sosai babu kayan aiki aciki.

Wasu mazauna garin na Gwanda dake karamar hukumar Danbatta sun bayyana mana cewa ‘yan siyasa suna musu alkawari zasu yi musu aiki idan sun zabesu amma har yanzu ba wani abu da suka musu a wannnan gari na Gwanda dake karamar hukumar Danbatta.

Wakilin dagacin garin na Gwanda Malam Sule Hamza Gwanda yace kiran ya zama wajibi duba da cewa kamar gwamnati ta mance da su.

Gwamnatin Kano ta tuhumi shugaban asibitin Rimingado

Gwamnan Jihar Borno ya kai ziyara asibitin kwararru na Umaru Shehu

Wakilin mu Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa al’ummar garin suna kira da ‘yan majalisa na yankin da Shugaban karamar hukumarsu da su mai da hankali wajen samawa jama’ar garin kayayyakin don bunkasa yanki da ma karamar hukumar Danbatta baki daya.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!