Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gobara ta ƙone shaguna 40 a Zawaciki

Published

on

Fiye da shaguna 40 sun ƙone a Unguwar Zawaciki, sakamakon gobarar da ta tashi da misalin ƙarfe 12:30 na daren Talatar makon nan zuwa wayewar garin yau Laraba.

Rahotonni sun bayyana cewa ana zargin gobarar ta faru ne sakamakon wutar lantarki.

Shagunan da suka ƙone sanadiyyar gobarar sun haɗa da na sayar da kayan masarufi da shagon sayar da kujeru da na Siminti da kuma shagon ɗinki.

Sai dai zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba a kai ga tattara alƙaluman dukiyar da gobarar ta laƙume ba kamar yadda Malam Garba Ibrahim Lahaula shugaban masu kasuwanci a yankin ya bayyana.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!