Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gobara ta hallaka mutane 7 yan gida daya a Kano

Published

on

Wata gobara da ta tashi a Unguwar Tudun Wada Birget da ke yankin karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano ta yi sanadiyyar konewar mutanen wani gida sakamakon rasa yadda zasu tseratar da rayuwarsu bayan tashin mummunar gobarar.

Rahotonni sun bayyana cewa, Gobarar ta tashi ne a daren jiya Lahadi.

A ganawar Freedom Radio da wasu shaidar gani da ido kan iftila’in, sun tabbatar da cewa mummunar gobarar ta tashi ne da misalin farfe goma sha biyu na dare jim kadan bayan an kawo wutar lantarki, wanda hakan yasa ake zargin wutar lantarkin ce musabbabin tashin gobarar.

Kimanin mutane takwas gobarar ta Kone a cikin gidan, inda mutane bakwai daga cikin su suka mutu nan take.

Wadanda suka rasun sun hada da Mai gidan da matarsa, sai kuma ‘ya’yan su mata biyar yayin da ita kuma ta takwas din yanzu haka an gargazaya da ita Asibiti domin ceto rayuwarta sakamakon konewar da ta yi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!