Labarai
Gobara ta kone Miliyoyin dukiya a Zariya
- Gobarar ta kona shaguna sama da dari kurmus, a kasuwar ‘yan Katako da ke Sabon garin Zaria a karamar hukumar Sabon Gari
- Shugaban kasuwar Alhaji Mohammed Ashiru ne ya bayyana
- tashin gobarar dai ya gagari jami’n da suke tsaron kasuwar, ta yadda suka kasa shawo kanta
- Mai magana da yawun hukumar kashe gobara yankin DSF Abubakar Ibrahim ya zargi rashin wadatattun kayan aiki na da nasaba da kasa shawo kan gobarar
- jami’an tsaron da suke gadin kasuwar ne suka sanar musu da tashin gobarar
Gobara ta yi sanadiyyar kona Miliyoyin dukiya, bayan da ta kona shaguna sama da dari kurmus, a kasuwar ‘yan Katako da ke Sabon garin Zaria a karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna a jiya.
Shugaban kasuwar Alhaji Mohammed Ashiru ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a garin Zaria.
Ya ce ‘jami’an tsaron da suke gadin kasuwar ne suka sanar musu cewa wutar lantarki ta yi bindiga inda ta fantsama cikin shagunan kasuwar ta kuma mamaye su.
Alhaji Mohammed Ashiru ya kuma ce, tashin gobarar ya gagari jami’n da suke tsaron kasuwar, ta yadda suka kasa shawo kanta, har sai da suka nemi agajin jami’an kashe gobara.
Sai dai a nasa bangaren mai magana da yawun hukumar kashe gobara da ke yankin na Sabon Gari DSF Abubakar Ibrahim ya zargi rashin wadatattun kayan aiki da suke fama da shi a matsayin abinda ya kara ta’azzara gobarar.
Rahoton: Madeena Shehu Hausawa
You must be logged in to post a comment Login