Labarai
Gobara ta lalata dukiya ta miliyoyin kudi a Kasuwar Sokoto

Wata gobara da ta tashi a tsohuwar kasuwar jihar Sokoto, da ake zargin ta samo asali sanadiyyar wutar lantarki, ta ƙone shaguna da dama.
Rahotonni sun bayyana cewa, Gobarar ta lalata kaya da dukiyoyi da darajarsu ta kai miliyoyin naira.
Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA shiyyar jihar ta ce, tawagarta ta kai daukin gaggawa ta garzaya wurin nan take bayan samun rahoton lamarin, tare da haɗin gwiwar Hukumar SEMA da Sashen Kashe Gobara.
NEMA ta kuma ce, haɗin gwiwar hukumomin ya taimaka wajen shawo kan gobarar tare da hana ta yaɗuwa zuwa sauran sassan kasuwar.
NEMA ta kara da cewa za ta ci gaba da fitar da ƙarin bayani game da lamarin yayin da ake samun sababbin bayanai.
You must be logged in to post a comment Login