Labarai
Gobara ta lalata shaguna 50 a kasuwar Fatima Simra da ke Dakata

Wata gobara da ta tashi da asubahin yau Juma’a ta lalata akalla shaguna 50 a kasuwar Fatima Simra da ke unguwar Dakata a nan Kano.
Shugaban kwamitin kashe gobarar kasuwar, Dauda Haruna Chula, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce gobarar ta fara ne da misalin karfe 4 na asubahin yau Juma’a.
Haruna Chula ya bayyana cewa mafi yawan shagunan da gobarar ta shafa na kananan ‘yan kasuwa ne da ke harkar sarrafa mai da kuma sake yin amfani da robobi da ledoji.
You must be logged in to post a comment Login