Connect with us

Labarai

Gobara ta lalata wani kamfanin sarrafa shinkafa a Kano

Published

on

Da tsakiyar ranar Alhamis ne gobara ta tashi a kamfanin da ke sarrafa shinkafa a unguwar sharaɗa da ke Kano, wanda yayi sanadiyyar lalata injin da ke bada wuta a kamfanin.

Shaidun gani da ido dai sun ce, injin yayi zafi sosai sai yayi wata ƙara, daga nan ne kuma sai hayaƙi ya gama wajan sai kuma wuta ta tashi.

Guda daga cikin ma’aikatan kamfanin ya shaidawa Freedom radio cewa gobarar ba ta lalata wani kaya ba, sai dai kawai ta lalata injin da ke baiwa kamfanin wuta.

“Ina zaune a gefen injin kawai sai naji wata ƙara,sai na tashi domin na ga menene sai na ga injin ne yake hayaƙi daga nan kuma sai na ga wuta na ci bal bal,kamar yadda dattijon da ke gudanar da sana’arsa a wajan”.

Sai dai hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin mai magana da yawun hukumar Saminu Yusuf Abdullahi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!