Labarai
Gombe: Ƴan sanda sun kama ƙasurgumin ɗan bindiga

Rundunar ‘yan sandan Jihar Gombe ta kama wani mutum mai suna Adamu Adamu mai shekaru talatin da ake zargin cewa ɗan bindiga ne da ke aikata ta’ addanci a tsakanin kan iyakar Najeriya da Kamaru.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar DSP Buhari Abdullahi, ne ya bayyana hakan ya na mai cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar 4 ga watan nan da muke ciki na Oktoba.
Ya ce, an kama shi ne bayan samun bayanan sirri da suka nuna cewa ya na tare da wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane.
Ya kuma ce, a yayin samamen da CSP Ali Madaki ya jagoranta a ƙarƙashin rundunar Operation Hattara, ‘yan sanda sun gano boyayyen wurin makamai a kusa da kauyen Wuro Biriji a Jihar Adamawa.
Ya ƙara da cewa, An kwato bindigogi kirar AK 47 guda biyu da harsasai 80 sai sarkoki da wuka da makulli da kuma jakunkuna hudu.
You must be logged in to post a comment Login