Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda ‘yan sanda suka kama wanda ake zargi da alaka da ‘yan bindiga a Katsina

Published

on

Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta kama wani tsohon shugaban riko na karamar hukumar Jibia Haruna Musa Mota da ake zargin yana da alaka da ‘yan bindiga  kuma yake aikata ta’asa a jihar.

Mai magana da yawun rundunar Gambo Isah ne ya bayyana haka ya yin zantawa da manema labarai.

Ya ce an kama tsohon shugaban riko na karamar hukumar ta Jibia ne sakamakon yadda yake taimaka wa wajen aikata ayyukan ta’addanci a jihar.

Ya kuma ce tuni an gurfanar da shi  a gaban kotu don girbar abin da ya shuka.

Rubutu masu alaka

Babban sufeton ‘yan Najeriya ya gana da manyan jami’an ‘yan sanda

Mun cafke masu safarar makamai a Katsina – ‘Yan sanda

An maida yaran da aka sace daga jihar Gombe zuwa Anambra – ‘Yan sanda

Rahotanni sun ce me yiwuwa rundunar ta kama Haruna Musa Mota ne sakamakon yadda aka ji muryarsa cikin wani  fefen  murya yana tattaunawa da ‘yan bindiga da suka sace daliban sakandieren kankara a watan Disamban shekarar da ta gabata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!