Connect with us

Labarai

Gombe: Yan sanda sun kama wasu mutane dauke da bindiga

Published

on

Rundunar ’yan sandan Jihar Gombe ta kama wasu mutane biyu dauke da bindiga a unguwar Orji kusa da Otal ɗin Jiemere.

 

Hakan  na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi ya fitar a jiya Laraba.

 

Sanarwar ta ce jami’an rundunar sun cafke mutanen ne yayin sintiri bayan sun hango alamar zargi a tare da mutanen, inda daya daga cikinsu ya yi yunkurin jefar da bindiga amma aka kwato ta.

Jami’in  ya ce bindigar na dauke da harsashi 

 

guda daya, kuma ana tsare da wadanda ake zargin yayin da ake ci gaba da bincike domin gano asalin bindigar da sauran alaka da ayyukan laifi.

 

Sanarwar ta ce rundunar ta jaddada kudurinta na yaki da laifuka tare da bukatar jama’a su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro hadin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanan sirri.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!