Labarai
Yan sanda sun tabbatar da sace mutane 5 a harin da yan bindiga suka kai Maitsauni
- Yan sanda sun kai dauki, sai dai maharan sun tsere gabanin zuwan su
- Bayan sace mutane 5 ‘yan bindiga sun kuma harbi wani a hannu
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce, wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari garin Maitsauni da ke yankin karamar hukumar Kankara tare da yin garkuwa da mutane biyar da kuma harbe mutum guda.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Gambo Isah, ya fitar.
SP Gambo Isah, ya ce, lamarin ya faru ne a jiya Lahadi, bayan da gun-gun maharan dauke da muggan makamai suka yi wa Kauyen na Maitsuni kawanya.
Haka kuma ya ce, ”Bayan zuwan maharan Kauyen ne kuma suka yi garkuwa da mutane biyar tare da harbin wani mutum a hannunsa wanda yanzu haka ya ke kwance a Asibiti yana karbar magani.”
A cewar sanarwar bayan rundunar ta sami labarin zuwan maharan, an aike da jami’an tsaro cikin gaggawa sai dai kafin su karasa Kauyen ‘yan bindigar sun tsere.
You must be logged in to post a comment Login