Labarai
Gwaman Abba Kabir ya taya mutanen Kano murnar shiga shekarar 2026

Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya taya al’ummar jihar murnar shiga sabuwar shekarar 2026.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da dubban al’umma suka taru domin murnar shiga sabuwar shekara a filin Mahaha, da ke yankin Kofar Na’isa a karamar hukumar Birni.
Haka kuma, a yayin taron, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga matasa da sauran al’umma da su guji yin duk wani abu da zai tayar da hankalin jama’a, tare da rungumar zaman lafiya da kaunar juna.
You must be logged in to post a comment Login