Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamna Abba Gida-Gida ya ɗaga likafar kakakin sa da naɗa sabbin muƙamai

Published

on

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da daukaka matsayin mai magana da yawunsa Sanusi Bature Dawakin Tofa daga babban sakataren yada labarai zuwa babban daraktan yaɗa labarai.

Wannan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na gidan gwamnatin jihar Kano Aliyu Yusuf ya fitar, ya ce nadin ya fara aiki nan take. Sanarwar ta kuma bayyana nadin wasu masu rike da mukaman siyasa da za su rike mukamai daban-daban kamar haka:

1. Hon. Rabi’u Saleh Gwarzo, Permanent Commissioner I SUBEB

2. Engr. Sarki Ahmad, Darakta Janar mai kula da ayyukan shiga yankunan karkara

3. Hon. Surajo Imam Dala, Darakta Janar na Kasuwanci

4. Dr. Dahiru Saleh Muhammad, Babban Sakataren Hukumar Kula da Makarantun Kimiyya da Fasaha

5. Abubakar Adamu Rano, mataimakin shugaban gidan rediyon Kano

6. Hajiya Hauwa Isah Ibrahim, Mataimakiyar Manajin Darakta, ARTV

7. Dr. Gaddafi Sani Shehu, Mataimakin Manajan Daraktan Kamfanin Raya Wutar Lantarki na Kano (KHEDCO).

Yayin da yake taya sabbin wadanda aka nada murna, Gwamnan ya umarci masu dauke da sabbin mukaman da su fara aiki nan take

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!