Labarai
Gwamna Abba Gida-Gida ya ƙaddamar da bayar da kayan noma ga mata
Gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da rabon kayan tallafin taki, iri, Dabbobi da injin ban ruwa na noman rani ga matan da suke yankin karkara domin samar musu da hanyoyin dogaro da kai.
Gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ne yayi wannan jawabin a yau juma’a yayin bayar da tallafin ga matan da suke yankin Falgore, a wani ɓangare na bikin rana mata ta duniya da ake yi.
Gwamna Yusuf ya ce yana fatan mata zasu ci gaba da jajincewa wajen gudanar da aiyukan su na yau da kullum.
Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatin sa zata ci gaba da fito da tsare-tsaren da zai tallafawa mata na dukkanin kananan hukumomi 44 dake faɗin jihar.
Wasu da suka anfana da tallafin sun ce suna fatan wannan abu da gwamnati tayi musu zai taimaka musu wajen gudanar da harkar noma.
Inda suka ƙara da cewa ba ƙaramin ƙaimi aka ƙara musu ba domin an magance musu matsalar da suke ciki na rashin kayan noma.
Gwamna Abba ya alƙawartawa al’ummar jihar Kano cewa gwamnatin sa zatayi duk mai yihuwa wajen taimakon al’ummar jihar domin rage musu raɗaɗin matsin rayuwa da ake fama da shi.
You must be logged in to post a comment Login