Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamna Abba ya bayar da tallafin kuɗi ga mata 1028 a kano

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da bayar da tallafin kuɗi naira dubu 20 ga mata 1028 na ƙananan hukumomi 44 dake jihar.

Gwamna Yusuf ya ƙaddamar da bayar da tallafin ne a ranar lahadi, a wani ɓangare na ci gaba da murnar ranar mata ta duniya da majalisar ɗinkin Duniya ta ware duk ranar 8 ga watan Maris a matsayin ranar mata ta duniya.

Gwamna Abba Kabir Yusuf, yayi kira ga matan da suka anfana da wannan tallafin da su mayar da hankali wajen gudanar da sana’o’in dogaro da kai.

Wasu matan da suka anfana da tallafin, sun bayyana farin cikin su, inda suka ce zasu mayar da hankali wajen gudanar da sana’o’in dogaro da kai domin wannan abu da gwamnati tayi musu ba ƙaramin ƙaimi zai ƙara musu ba.

Gwamnan ya ce gwamnatin sa zata ci gaba da fito da tsare-tsaren da zasu tallafawa Al’ummar jihar Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!