Labarai
Gwamna Abba Gida-Gida ya bayar da Garatuti ga ƙananan ma’aikata 5000
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da bayar da kudin garatuti ga ma’aikatan gwamnati da suka kammala aiki su dubu biyar, inda gwamnan yayi kira ga dukkannin wa’inda suka karɓi kuɗin da suyi anfani da shi ta hanyar da ya da ce
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce abin alfahari ne yau domin rana ce da gwamnatin kano ta fara biyan ƙananan ma’aikata kuɗin garatutin su domin sun shafe shekaru da kammala aiki amma hakkin du bai fito ba wanda hakan baiyi daidai da tsarin mulki ba.
Haka kuma gwamnatin ta ce ta zagaya kananan hukumomin jihar Kano 44 domin fito da dukkannin wa’inda duka kammala aiki domin biyan su hakkin su.
Gwamnan ya kuma ce wasu daga cikin wa’innan mutane da hakkin ya ki fitowa akwai wa’inda sun rasu kuma yanzu haka iyalan su na cikin mawuyacin hali, adan haka dole gwamnati tayi duba da irin wa’innan iyalai domin biyan du hakkin su
Haka kuma gwamna Abba yayi kira ga dukkannin wa’inda suka karɓi wannan kuɗin su 5000 da suyi abin da ya da ce da abin da aka basu wajen yin sana’a domin kulawa da iyalai su.
Yanzu haka gwamnatin kano ta ce zata ci gaba da bayar da wannan kuɗin ga dukkan ma’aikanta suka kammala aiki domin zuwa su gudanar da kaduwancin da zai riƙe rayuwar su da iyalan su
You must be logged in to post a comment Login