Connect with us

Labarai

Gwamna Abba Kabir ya nada Sarkin Karaye a matsayin Jagoran Mahajjata

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya nada mai Martaba Sarkin Karaye, Alhaji Dakta Muhammad Mahraz Karaye, a matsayin shugaban Kwamitin jagorantar mahajjatan Kano na bana domin kyautata tsarin tafiya da gudanar da ayyukan alhazai a ƙasar Saudiyya.

 

Kwamitin zai kasance cibiyar hada-hadar gudanar da ayyuka  da suka shafi aikin Hajji a ƙasar Saudiyya, tun daga farko har zuwa kammala ibadar. 

 

Bayanin hakan na kunshe ta cikin wata sanarwa da Sulaiman Dederi, jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Alhazai ya fitar.

 

Babban aikin kwamitin shi ne tabbatar da ingantaccen tsari da dai-daito da kuma kula da walwalar alhazan Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!