Labarai
Gwamna Abba Kabir ya sauya sunan kwalejin wasanni zuwa sunayen yan wasa 22 da suka rasu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sauya sunan kwalejin horas da matasa harkokin wasanni zuwa sunayen tawagar ‘yan wasan Kano 22 da suka rasu a kan hanyarsu ta komawa gida daga gasar ƙasa a watan jiya na Mayu.
Yayin wani biki a gidan gwamnatin jihar, Gwamna Abba ya sanar cewa daga yanzu za a dinga kiran kwalejin Kano State Sports Institute da sunan Kano State 22 Athletes Sports Institute domin tunawa da su.
Kazalika, ita ma hukumar harkokin wasanni ta sauya suna zuwa Kano State 22 Athletes Sports Commission.
Gwamnan ya bayar da sanarwar ne lokacin da wata tawagar wakilai ta uwargidan shugaban ƙasa Remi Tinubu ta kai ziyarar jaje, inda ta bayar da gudummawar naira miliyan 110.
You must be logged in to post a comment Login