Labarai
Gwamna Abba Kabir ya shirya gabatar wa majalisar dokoki kasafin 2026

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince wa Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da ya gabatar mata da kasafin kuɗin shekarar 2026 da ke tafe.
A zaman ta na yau Litinin ne shugaban majalisar Jibril Isma’il Falgore, ya karanato wasiƙar da gwamnan ya aika musu.
A nasa bangaren, shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Husaini Dala, ya yi karin haske kan wasiƙar gwamnan tare da gabatar da kudirin haɗin gwiwa na samar da hanya a kananan hukumomin Dala da Birni.
Gwamnan zai gabatar wa da majalisar kasafin kuɗin a ranar Laraba 19 ga watan Nuwamba 2025.
You must be logged in to post a comment Login